Babban magana: EFCC ta kama dan damfara a fadar shugaban kasa

Legit Hausa
Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta kama wani dan damfara mai su a Abdulrauf Illyasu bisa zargin damfarar jama'a a tsakanin fadar Shugaban kasa, Abuja.
An tattaro cewa Illyasu ya nemi ofishinsa a wajen da ke kallon dakin taron na shugaban kasa wato 'Presidential Banquet Hall' domin aiwatar da ayyukansa na damfara.
Binciken EFCC ta nuna cewa yayi nasarar damfaran Babban Darektan kamfanin Galaxy Investment, Babagana Dalor kudi naira miliyan 500.
Hakazalika Dalor na a karkashin binciken EFCC bisa zargin gudanar da shirin rufa-ido.
Illyasu har ila yau ya damfari kamfanin Union and Allied Engineers Ltd. naira miliyan 70.
Suran wadanda ya damfara sun hada da Excel Technology Ltd., wacce tayi hasaran naira miliyan 50 ga madamfarin, Arabo and Co. Ltd., naira miliyan 50; Crystal gate Ltd., naira miliyan 25; Diamond Global Fencing, fiye da naira miliyan 27 da wasu da dama.
An tattaro cewa mai laifin yayi nasaran damfaran su ne ta hanyar gabatar dasu ga wasu gwamnonin jihohi.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post