Duba nasara da Umar Namashaya ya fara samu a shirin sulhu tsakanin Gwamnatin Kebbi da Aisha

An kama hanyar nassara a sulhu da ake shiryawa tsakanin Gwamnatin jihar Kebbi da Nasiru Jatau Yauri tare da matarsa Aisha Zakari wanda tsohon shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo a jihar Kebbi Alhaji Umar Namashaya Diggi ya assasa.

Mujallaar isyaku.com na da tabbacin cewa a matakin tuntuba da neman a yafe wa juna kuma a rungumi sulhu, Umar Namashaya Diggi, ya yi nasarrar tuntuban Nasiru Jatau, wanda ya bukaci a bashi lokaci domin ya yi shawara da sauran danginsa, tare da yan uwa da sauran ahalinsa da lamarin ya shafa.

Hakazalika, majiyar mu ta ce Nasiru Jatau, ya bukatar lokaci har yau, domin ya tuntubi matarsa, surukansa da danginta kan lamarin.

Idan baku manta ba, rundunar hukumar DSS na jihar Kebbi ta kama Nasiru Jatau tare da matarsa Aisha Zakari har da babban dansu Babangida daga garin Yauri na jihar Kebbi, aka tsare Nasiru tare da matarshi Aisha bisa zargin cewa Aisha ta aika sakon TEXT daga wayar salularta inda ta tsoratar tare da tayar wa Gwamnan jihar Kebbi hankali.

Sakamakon haka DSS ta gurfanar da Aisha a gaban wata Kotun Majistare a garin Birnin kebbi, yayin da Lauyan Aisha da mijinta Nasiru Jatau, watau Barista A.A Fingilla ya maka Gwamnatin jihar Kebbi a wata babban Kotun tarayya yanna neman DSS da Gwamnatin jihar Kebbi su biya Aisha da mijinta Nasiru Naira Miliyan dari biyar sakamakon cin zarafi da DSS da Gwamnatin jihar Kebbi suka yi masu.

Bisa wannan dalili ne Umar Namasha Diggi, ya assasa wani shiri da zai kai ga sulhu tsakanin bangaren Gwamnatin jihar Kebbi da kuma Nasiru tare da matrsa Aisha, marmakin matakin shari'a ganin cewa Gwamnati na jayayya ne da talakanta a Kotu.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari