Kama Aisha da mijinta Nasiru: Jama'a sun yi na'am gwamnatin Kebbi ta yi sulhu marmakin shari'a

Jama'a a jihar Kebbi da ma arewacin Najeriyya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan rikicin da ke tsakanin Gwamnatin jihar Kebbi da talakanta wata mata mai shayar da jaririya yar wata biyar a Duniya bisa zargin cewa ta tayar wa Gwamnan jihar Kebbi hankali bayan ta aika masa sakon TEXT daga wayar salula.

Sakamakon wata tambaya da isyaku.com ya wallafa a shafin sada zumunta na Facebook, ya nuna cewa jama'a da dama sun goyi bayan wani yunkurin sulhu tsakanin bangarorin guda biyu, da wani tsohon shugaban karamar hukumar mulki ta Kalgo a jihar Kebbi, Alhaji Umar Namashaya Diggi ya assasa kuma yake kokarin ganin hakan ya tabbata tsakanin bangarorin biyu.

Haka zalika, ra'ayin jama'a da isyaku.com ya tattaro a cikin garin Birnin kebbi, wanda ya hada da jin ra'ayin jama'a kama daga teburin masu shayi, masu dafa indomie, masu sayar da waina, yan acaba, tuntuba ta wayar salula, jin ra'ayin mutane a titi da sako sako na garin Birnin kebbi, jama'a masu rinjaye sun goyi bayan a yi sulhu tsakanin Gwamnati da Aisha tare da mijinta Nasiru Jatau.

Wani magidanci mai mata biyu kuma dan kasuwa da baya son a ambaci sunansa, wanda isyaku.com ya hadu da shi a wajen cin waina, ya ce " Idan ka lura da ka dauko wannan zance, mutane da dama sun yi tsaki. A gani na gaskiya Gwamnati ta yi kuskure har ta shiga Kotu da wannan mata da ke shayar da jaririya, kuma talaka. Abin da nike son Gwamna Atiku ya sani shine, wallahi ko da Gwamnati ta yi nassara a wannan shari'a girma ya fadi, haka zalika ko da Aisha ce ta yi nassara a shari'ar girma dai ya fadi, tunda Gwamnati ce ke karar talaka kuma mace wacce ke renon jaririya".

"Kamata ya yi Gwamna ya zama uban kowa kuma mai hakuri da talakawansa. Wannan abu ne da za a iya warware shi cikin ruwan sanyi bayan DSS sun yi bincike sun gano wanda ke da alhakin tura sakon TEXT da aka ce an tura masa da ya bata masa rai. Daga wannan mataki kuma tunda talaka ne aka gano cewa ana zargin ya aika wannan sako , ai sai a umurci basaraken yankinsu ya gargade ta tare da jan kunne ba wai ayi irin wannan kame kame ba da nuna kaefin hukuma".

Bayan hukummar DSS ta gurfanar da Aisha a gaban wata babban Kotun Majistare mai daraja ta daya a garin birnin Kebbi bisa tuhumar tayar wa Gwamnan jihar Kebbi hankali ta hanyar aika masa sakon TEXT daga wayar salula, Aisha ta musanta haka a gaban Alkalin kotu.

Sai dai Lauyan Aisha, Barista A.A Fingilla, ya maka Gwamnatin jihar Kebbi tare da hukumar DSS a gaban wata babban kutun tarayya a garin Birnin Kebbi yana neman a biya Aisha tare da mijinta Nasiru Naira Miliyan dari biyar bisa abin da ya ce "sakamakon cin zarafi da Gwamnatin jihar Kebbi ta sa hukumar DSS tayi ma Aisha da Nasiru bayan an tsare su har kwana goma sha uku (13)".

Ko ma da wace aka kwana, rana bata karya sai dai uwar diya ta ji kunya. Jama'a sun zuba ido domin su gan ikon Allah a jihar da Gwamnati ta kai yara Kurkuku domin sun yi zanga zanga kan lamarin wutan lantarki da ya shafi duk mazauni garin Birnin kebbi, kuma yanzu ta ke shari'a a Kotu da mace, talaka matar aure mai shayar da jaririya yar wata biyar a Duniya.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari