Yadda bera ya sanya 'yan majalisa gudun famfalaki a fadar shugaban kasar Amurka

Legit Hausa
A ranar Talatar nan da ta gabata ne 'yan jarida suka ga wani abin mamaki, yayin da wani bera ya fado daga saman rufin fadar shugaban kasar Amurka wato 'White House'.
Beran dai ya fado akan cinyar wani wakilin jaridar NBC ne dake fadar shugaban kasar mai suna Peter Alexander, da misalin karfe 10:45 na safe.
Wasu daga cikin 'yan jaridar sun ranta ana kare, yayin da wasu kuma suka yiwa beran tara-tara domin su kama shi. Beran dai ya shiga ta wata kofa ne ya gudu abinsa, inda masu kaman shi din suka hakura bayan ya bace musu.
An dinga sanya hoton wannan bera a kafar sadarwa ta zamani, inda ya zama abin magana ga mutane.
Beraye, gafiyoyi, da kyankwaso dama sun jima da cika fadar shugaban kasar, domin kuwa a shekarar da ta gabata wani bera ya samu shiga fadar shugaban kasar, abinda ya saka aka sanya masu korar beraye a kowanne mako a fadar shugaban kasar.
DAGA ISYAKU.COM

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post