Zaben APC: Yadda mutanen Sakaba suka gudanar da zanga zanga a Birnin kebbi

Wasu mutane daga karamar hukumar Sakaba da ke kudancin jihar Kebbi, sun gudanar da zanga-zangar lumana a garin Birnin kebbi domin nuna bacin ransu dangane da yadda zaben fitar da gwani na mukamin Chiyaman da Kansiloli ya gudana a karamar hukumar Sakaba ranar Asabar.

Masu zanga-zangan sun rike kwalaye dauke da rubuce rubuce da ke kira ga jam'iyar APC ta yi adalci kuma ta gudanar da zabe a karamar hukumar.

A daya daga cikin rubutun da ke a kwali da masu zanga-zanga suke rike da su, an rubuta " APC muna son a yi zabe ba wai dauki ka dora ba a Sakaba" wani kwalin kuwa yana dauke da rubutun " Ba a yi zaben fidda gwani ba a Sakaba"  da "A bamu Kwamiti mu je Sakaba a yi zabe" da sauransu.

KALLI BIDIYO:An gudanar da zanga zangar ne a bakin benen Akoko da ke kan hanyar gidan talabijin na jihar Kebbi, KBTV da misalin karfe 2:09 na rana, daga bisani masu zanga -zangar suka shiga motocinsu suka hau hanya suna rike da wadannan kwalaye kuma suka bi ta gidan Gwamnati, ba tare da sun tsaya ba suka wuce.

An gudanar da zabukan fitar da gwani a jam'iyar APC a jihar Kebbi ranar Asabar da ta gabata, amma lamarin ya haifar da kace-nace tare da nuna wa juna yatsa tsakanin yayan jam'iyar APC tare da samun rahotanni da suka ci karo da juna dangane da sahihancin yadda zaben ya gudana a wasu kananan hukumomi.

Wasu daga cikin mutanen da suka nuna rashin jin dadinsu dangane da lamarin na karamar hukumar Sakaba sun hada da, Alh. Aliyu Diri, Alh. Bala Sakaba, Alh. Tela Chiyaman Jan Birni Ward,, Chiyaman Tanko, Mayake Dokabare, Alh. Emada, Sale Garba, da Ado M.Bala, daga cikin dimbin jama'a da suka halara domin mika kokensu ga uwar jam'iyar APC na jihar Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari