Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujeran wani Sanatan APC ta ba PDP


Legit  Hausa

Kotun zaben yan majalisar dattawa dake Ado-Ekiti, birnin jihar Ekiti ta soke nasarar kakakin majalisar dattawa, Sanata Dayo Adeyeye, na jam'iyyar All Progressives Congress APC, a zaben 23 ga Febrairu, 2019. Bayan soke nasararsa, kotun ta alanta abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Sanata Biodun Olujimi, matsayin wacce ta lashe zaben na halas.

A watan Febrairu, hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta alanta Adeyeye a matsayin wanda ya lashe zaben. Hakan ya sa Bidun Adeyeye ta garzaya kotu domin kwato hakkinta. Ta bayyanawa kotu cewa ita ta samu rinjayen kuri'u amma INEC danne mata hakkinta.

Olujimi ta bukaci kotun ta soke nasarar abokin hamayyarta, Dayo Adeyeye, kuma a gudanar da sabon zabe. Yayinda ake yanke hukuncin, kwamitin alkalan karkashin jagorancin, Alkali D.D Adeck, ya soke zaben wasu yankunan mazabar kuma ya alanta Biodun Olujimi ta PDP matsayin wacce ta lashe zaben. A karshe, kotu ta ce Olujimi ta samu kuri'u 54,894, yayinda Sanata Dayo Adeyey ya samu kuri'u 52,243.

A wani labarin mai kama da haka, Jam'iyyar APC ta ce zata daukaka kara akan nasarar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa da kotu ta tabbatar. Shugaban jam'iyyar APC na jihar Enugu, Ben Nwoye, a tattaunawar da yayi da kamfanin dillancin labarai akan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta yanke ne ya tabbatar da hakan.

'Yar takarar kujerar sanata ta yankin yammacin Enugu, Juliet Ibekaku-Nwaguwu ta jam'iyyar APC ta tunkari kotun sauraron kararrakin zaben da korafi bayan an bayyana Ekwerwmadu a matsayin wanda ya lashe zaben.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post