Gwamna Bagudu da mutanen Abacha sun saci Biliyoyin Daloli a Gwamnati – Inji Adoke

Daga Legit Hausa
Mun samu labari cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta gano wasu makudan dalolin kudi da aka sace daga asusun Najeriya a lokacin da tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha ya na mulki.
Tsohon Ministan shari’an Najeriya, Mohammed Bello Adoke SAN, ya bayyana cewa Marigayi Sani Abacha ya saci kudin gwamnati a lokacin da ya ke mulkin Najeriya daga shekarar 1993 zuwa 1998.
Mohammed Bello Adoke ya ke cewa Sani Abacha da ‘Ya ‘yansa da ‘Yanuwansa sun yi amfani da wasu akawun din kasashen waje wajen sace kudin Najeriya har bayan shugaban ya bar kan mulki.
Tsohon Ministan na gwamnatin Jonathan yake cewa mutanen Abacha sun jefa kudin Najeriya zuwa irin su kasashen Luxembourg, Liechtenstein, Channel Island of Jersey, da kuma kasar Faransa.
Bello Adoke ya kara da cewa Iyalin Abacha sun wawuri kudin Najeriya sun ajiye har a Switzerland da Birtaniya. Enrico Monfrini shi ne Lauyan kasar wajen da ya bankado wannan asiri inji Adoke.
Ministan shari’ar na-da, ya ce Iyalan Sani Abacha sun bace da Dala biliyan 1.3 bayan wasu kudin da su ka boye a kasashen Turai. Adoke ya bayyana wannan ne a wani littafinsa da ya rubuta.
A wannan littafi mai suna “Burden of Service” da ya shiga hannun ‘yan jarida, tsohon Ministan ya ke cewa Najeriya ta yi kokari wajen dakile mafi yawan kudin da tsohon shugaban ya sace.
Lauyan ya bayyana yadda Yaron Sani Abacha, Mohammed, ya zama cikas ga gwamnatin Janar Abdulsalami Abubakar wanda ya yi yunkurin karbe wasu kudi da gwamnatin Abacha ta wawura.
Littafin ya ke cewa Abacha ya yi amfani da Danginsa da Sanata Sanata Atiku Bagudu wajen sace dukiyar Najeriya. Yanzu dai Atiku Bagudu shi ne shugaban gwamnonin APC mai mulkin Kebbi.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post