Shekaru biyu bayan
karewar wa'adin shugaban kasar Amurka na 44 a tarihi, Barack Obama, wata
shahararriyar mai daukansa hotuna, Callie Shell, ta saki wasu zafafan
hotunansa da babu lallai idanu sun taba kai wa gare su.
Tarayyar Callie Shell da Obama ta faro ne tun a shekarar 2004 a yayin da
yake neman takarar kujerar Sanata kamar yadda tarihi ya tabbatar.
A wani sabon littafi da ta wallafa kamar yadda jaridar Independent ta
bayar da tabbaci, Shell ta hikaito rayuwar Obama tare da iyalansa, tun
yayin da ya kasance dan majalisa, dan takarar shugaban kasa da kuma
bayan ya kasance shugaban kasar Amurka na farko da ya fito daga tsatson
bakar fata kuma mai asali a nahiyyar Afirka.
Kwararriyar mai daukan hoton ta saki hotunan tsohon shugaban kasa Obama
tare da matarsa, Michelle da kuma 'ya'yansa mata biyu; Malia da Sasha.
Read more: https://hausa.legit.ng/1261114-wasu-hotunan-tsohon-shugaban-kasa-barack-obama-tare-da-iyalansa-da-baku-taba-gani-ba.html
Legit Hausa
Obama yana taya yayansa wanke wanke |
Shekaru biyu bayan karewar wa'adin shugaban kasar Amurka na
44 a tarihi, Barack Obama, wata shahararriyar mai daukansa hotuna, Callie
Shell, ta saki wasu zafafan hotunansa da babu lallai idanu sun taba kai wa gare
su.
Tarayyar Callie Shell da Obama ta faro ne tun a shekarar
2004 a yayin da yake neman takarar kujerar Sanata kamar yadda tarihi ya
tabbatar.
A wani sabon littafi
da ta wallafa kamar yadda jaridar Independent ta bayar da tabbaci, Shell ta
hikaito rayuwar Obama tare da iyalansa, tun yayin da ya kasance dan majalisa,
dan takarar shugaban kasa da kuma bayan ya kasance shugaban kasar Amurka na
farko da ya fito daga tsatson bakar fata kuma mai asali a nahiyyar Afirka.
Kwararriyar mai
daukan hoton ta saki hotunan tsohon shugaban kasa Obama tare da matarsa,
Michelle da kuma 'ya'yansa mata biyu; Malia da Sasha.
Obama yayin wata hira ta wayar Salula da yan Jarida a 2008 |
Kallon Talabijin tare da iyalinsa gabanin wani taron yakin neman zaben 2008 |
Obama ya tsaya tsaf, ya shaki iska kafin yin takun karshe na ficewa daga Fadar Gwamnati a matsayin shugaban kasar Amurka na 44 |
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN