Rayuka sun baci: Zan jingine kariyana domin a bincike ni, inji Osinbajo


Legit Hausa

Matamakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo yace zai jingine kariyar da kundin tsarin mulki ta bashi domin a bincike shi. “A yan kwanakin da suka gabata, wasu bayanan karya na ta yawo a kafofin watsa labarai akaina, wanda wata kungiyar mahasadda ke ta kitsawa,” ya wallafa a shafin twitter.

“Labarin na bata da suna da batarwar da wannan kungiya ta shirya na ta yawo kafofin sadarwa ba tare da suna ba. “A yau na bayar da umurnin fara daukar mataki na doka akan wasu mutane biyu, daya Timi Frank da kuma wani Katch Ononuju, wadanda suka sanya sunayensu akan labaran karyan.

“Zan jingine kariyar da kundin tsarin mulku ta bani domin ba kotu damar hukunci akan wannan iikirari na batanci da karya," inji Osinbajo. Timi Frank, tsohon mataimakin sakataren labaran jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayi zargin cewa hukumar tattara kudaden shiga na tarayya (FIRS) ta bayar da naira biliyan 900 ga mataimakin Shugaban kasa don kamfen din zabe, zargin da tuni hukumar harajin ta karyata. Amma tuni Frank yayi martani inda ya bukaci hukumar FIRS ta daina yaudarar yan Najeriya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post