Yanzu-yanzu: Wata daya bayan nada ministoci, Buhari yayi sauye-sauye cikin Ministocinsa


Legit Hausa

Rahoton da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya canza daya daga cikin ministocinsa, Barista Festus Keyamo. Festus Keyamo wanda Buhari ya nada karamin ministan Neja Delta ya rasa kujeransa amma an mayar da shi matsayin karamin ministan kwadago da daukan aiki.

 Legit.ng ta samu wannan labari ne daga bakin Festus Keyamon da kansa da yammacin nan inda ya bayyana wasikar a shafin ra'ayi da sada zumuntarsa ta Tuwita.

Yace: "Yanzunnan aka mayar da ni ma'aikatar kwadago domin aiki da tsohon babban yayana, Chris Ngige."

Hakazalika, shugaba Buhari ya mayar da Tayo Alasoadura ma'aikatar Neja Delta matsayin karamin minista. TheCable ta ruwaito cewa an samu rikici tsakanin Festus Keyamo da Godswill Akpabio ne a ma'aikatar ta Neja Delta.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post