Wani mutum ya fille kan dan achaba, ya kuma cire kayan cikinsa a jihar Neja

Legit Hausa
Rundunar yan sanda sun kama wani da ake zargin matsafi ne, Tunde Tayo na Ungwan Roka, Maitumbi, Minna a karamar hukumar Bosso da ke jihar Niger, bisa zargin kashe wani mutum sannan ya binne shi a kangon gidansa bayan ya cire masa kai.
An kama Tayo ne bayan ya fille kan mutumin wanda ya kasance dan achaba, sanan ya cire zuciya da kayan cikisa a yankin Crystal FM da ke Maitumbi.
Newtelegraph ta ruwaito cewa matashin da aka kashe mai shekara 25 a duniya, Abdullahi Salle, ya kasance dan achaba.
An tattaro cewa jami’an yan sanda da ke reshen Maitumbi ne suka kama Tayo mai shekara 30 bayan ya kashe dan achaban wanda ya kasance dan Ungwan Rama domin yayi asiri dashi.
Da yake amsa tambayoyi, mai laifin yayi ikirarin cewa yana gyara ciyayin da suka tashi ne a gini kafin aka kama shi.
Bayan an ci gaba da bincike sai aka gano cewa mai laifin ya binne gawar Salleh a cikin wani babban rami da ke kusa da gidansa.
Mai laifin yace ya yaudari mutumin zuwa kangon gininsa da ke Ungwan Roka, inda ya aikwatar da mummunan ta’asar.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post