Hukumar EFCC ta kama wasu manyan jami’an gwamnatin Sokoto 2 kan zargin karkatar da albashin ma’aikata

Legit Hausa
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen jihar Sokoto, a ranar Juma’a, 13 ga watan Satumba, ta kama Abdullahi Sa’idu, Darakta Janar na hukumar tsaro da Bashar Dodo-Iya, akawun hukumar kan zargin karkatar da naira miliyan 10 da ya kamata a biya albashin ma’aikata.
An kama masu laifin su biyu wadanda suka kasance mambobin kwamitin biyan jami’an tsaron a Sokoto, biyo bayan wata kara na hadin gwiwa dauke da sa hannun mambobin hukumar 39 zuwa ga hukumar, kan zargin cewa an rike masu albashin watanni uku ba tare da kowani dalili ba.
Sun ci gaba da zargin cewa masu laifin sun ki biyansu albashi sannan sun karkatar da kudin zuwa ga amfanin kansu.
Binciken farko ya tabbatar da zargin cewa masu laifin sun karkatar da kudin. Za a gurfanar da su a gaban kotu da zaran an kammala bincike.
Hukumar EFCC ta kama wasu manyan jami’an gwamnatin Sokoto 2 kan zargin karkatar da albashin ma’aikata
A wani labarin kuma mun ji cewa hukumar kula da kudade ta NFIU ta soma gudanar da bincike a kan asusun bankin shugaban majalisar dattawa Lawan Ahmad da mataimakinsa Ovie Omo-Agege.
NFIU ta fara gudanar da wani bincike game da asusun bankin da shugabannin majalisar dokokin ke ajiyar kudi.
Wadanda wannan binciken ya shafa sun hada da; Shugaban majalisar dattawa Lawan Ahmad, kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, mataimakin kakakin majalisar wakilai Idris Wase da sauran masu rike da mukamai a cikin majalisun biyu.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN