Wani barawo ya mutu bayan kan shi ya makale a burgler na tagan gidan da ya je sata


Wani matashi ya yi mumunar karshe bayan ya mutu yayin da ya je sata a cikin Mujami'ar Prestige a unguwar Arepo da ke yankin Awori cikin Abule Egba a birnin Ikko watau Lagos ranar Talata.
 
Bayanai sun nuna cewa wannan barawo ya shiga Mujami'ar ne da dare domin ya yi sata, amma sai kanshi ya makale a karafan tsaro da aka sa a Tagan Mujami'an, sakamakon haka ya shake har ya mutu.
 
Rahotanni sun ce an taba yin sata har sau biyu a wannan Mujami'a a bana inda aka dauke na'urar sauti daga bisani kuma a sata na biyu aka sace na'urorin lantarki. 
 
Sakamakon haka ya sa shugabannin Mujami'an suka yanke hukuncin sa karafan tsaro (burgler proof) wanda kuma yin haka ya yi sanadin kamawa tare da kashe barawon da ya addabe Mujami'an. 


 


DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post