Tap di jan! An zartar da dokar ba mahaifi dama ya auri diyarsa a kasar Iran


Legit Hausa

Majalisar kasar Iran ta sanya hannu akan wata doka da zata kare hakkin yara kanana ciki kuwa hadda baiwa wani mutumi damar auren 'yarsa da ya dauko riko duk kuwa da cewa shekarunta 13 a duniya.

Sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasar sun yo caa akan wannan doka da majalisar kasar ta sanyawa hannu, wacce zata dinga baiwwa iyaye maza damar auren 'ya'yansu mata da suka dauko riko.

Manyan kasar ta Iran, sun duba wannan doka da majalisar ta aika musu sun kuma kwatanta ta da hallacinta a addinin musulunci, amma har yanzu ba ta gabatar da hukunci a kai ba. A kasar Iran yarinya 'yar shekara 13 za ta iya aure amma idan alkali ya bayar da dama. Zuwa yanzu dai auren 'ya'yan riko bai hallata ba a kasar.

Yara mata 42,000 ne wadanda suke tsakanin shekara 10 zuwa 14 suka yi aure a shekarar 2010, kamar yadda shafin yanar gizo na Tabnak ya wallafa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post