Yan majalisar dokokin jihar Sokoto na APC sun lallasa yan PDP a kotun zabe


Legit Hausa

Kotun sauraron kararrakin zabe na majalisar dokokin jiha da ke zama a Sokoto, a ranar Laraba, 25 ga watan Satumba, ta jaddada zaben mambobin majalisar dokokin jihar Sokoto, da ke wakiltan mazabar Gada ta yamma, Hon. Kabiru Dauda da mai wakiltan mazabar Rabah, Hon. Abubakar Zakari.

Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben ranar 9 ga watan Maris, 2019, a mazabar Gada ta yamma, Hon. Garba Yakubu Tsitse ne ya kalubalanci kaddamar da Dauda na jam’iyyar All Progressives Congress ( APC) a matsayin wanda ya lashe zaben.

Hakazalika, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a zaben mazabar Rabah, Hon. Abubakar Gandi ya kalubalanci kaddamar da Zakari na APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

A kararrakinsu, yan takarar sun yi zargin cewa wadanda ake karan basu samu mafi yawan kuri’un da aka kada bisa doka ba, sannan cewa zaben bai gudana daidai da dokar zabe na 2010 ba, da kuma tsarin jadawalin INEC na zaben 2019 ba.

Da yake yanke hukunci, Shugaban kotun zaben, Justis Ubale Yusuf, yace dukkanin kararrakin basu da inganci. Yayi bayanin cewa masu karar sun gaza tabbatar da shari’arsu. Don haka Justis Yusuf yayi watsi da kararrakin.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN