Boko Haram: Yi wa doka da'a ya sa Jonathan ya fasa tsige gwamnonin wasu jihohi 3 na Arewa

Legit Hausa
Tsohon ministan shari'a kuma lauyan koli na kasa, Mohammed Adoke, ya yi karin haske dangane da dalilai da suka sanya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya fasa sauke gwamnonin wasu jihohin Arewa uku duk da an kaddamar da dokar ta baci a sanadiyar ta'addancin kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.
Ana iya tuna cewa, a yayin da ta'addancin Boko Haram ya ta'azzaa, tsohon shugaban kasa Jonathan a ranar 13 ga watan Mayun 2013, ya shimfida dokar ta baci a wasu kananan hukumomi na jihohin Adamawa, Yobe da kuma Borno.
Duk da wannan hukunci da tsohon shugaban kasar ya dauka, bai sauke gwamnonin jihohin ba da kuma shugabannin kananan hukumominsu, lamarin da ya janyo masa suka gami da caccaka a tsakanin makarabban gwamnatinsa da kuma mambobin jam'iyyar sa ta PDP.
A yayin da wannan hukunci ya bai wa jam'iyya mai ci a wancan lokaci damar tsige gwamnonin jam'iyyar APC, tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi watsi da muradinsu tare da cewa aiwatar da hakan ya sabawa dokar kasa da kundin tsari mulki.
Tsohon ministan shari'a kuma lauyan koli na Najeriya, Mohammed Adoke, shi ne ya bayyana hakan cikin wani sabon littafi da ya wallafa mai taken tuna baya a kan nauye-nauyen da ke kan tsaffin lauyoyin koli na Najeriya.
A cewar Adoke, Jonathan ya hau kujerar naki ta ribatar dokar ta baci da ya shimfida wajen tsige-tsige gwamnonin uku, duk da shan suka da caccaka ta manyan kusoshin gwamnatinsa da suka hadar da ministoci da magoya bayan jam'iyyar PDP.
Tsohon ministan ya ce ya shawarci Jonathan a kan sauke gwamnonin uku tun da babu wata doka a kasar da ba shi damar aiwatar da hakan.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Reported by ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
LATSA NAN 

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

Facebook.com/isyakulabari