Kotu ta bayar da belin Aisha bayan DSS ta gurfanar da ita bisa zargin yi wa Gwamnan Kebbi barazana

Da karfe 12:46 na ranar Litinin 16 ga watan Satumba 2019 rundunar Department of State Services DSS na jihar Kebbi ta gurfanar da wata mata mai suna Aisha Zakari bisa tuhumar laifuka da suka shafi yi wa Gwamnan jihar Kebbi barazana a wayar salula.

Bayan da Kotu ta karanta wa Aisha laifuka da ake tuhumarta, wanda Rajistira na Kotun Majistare mai daraja na 1 a garin Birnin kebbi ya karanta mata, Aisha bata amsa laifinta ba. Sakamakon haka Lauya mai wakiltar Aisha Barista Bashir Umar ya gabatar wa Kotu bukatar a bayar da belin Aisha bayan ya karanto wasu ayoyin doka da misalansu na dalilin da ya sa yake neman Kotu ta bayar da belin Aisha ta la'akari da cewa tana shayar da karamar yarinya yar wata biyar a Duniya.Lauya mai wakiltar hukumar DSS D.I Namata, ya bukaci kada Kotu ta bayar da belin Aisha. Amma bayan wata yar gajeruwar muhawara a kan dalilai da suka sa ya kamata Kotu ta bayar da belin Aisha kamar yadda Layanta Barista Bahir ya nace Kotu ta yi bayan ya kara zakulo wasu dalilai tare da misali da ayoyin doka da kuma irin wadannan matsaloli da suka gabata a fuskar doka.

A muhawarar Lauyan hukumar DSS, Barista Namata ya bukaci kada Kotu ta bayar da belin Aisha domin kada ta tsere ko ta yi katsalandan ga bincike da suke ci gaba da yi. Amma Barista Bashir ya ce babu yadda Aisha zata tsere wa Kotu ko hukumar DSS idan Kotu ta bayar da belinta.

A nashi martani, Alkalin Kotun ya gamsu cewa laifin da ake tuhumar Aisha lafi ne da za a iya bayar da beli,kuma ya gamsu da duk tsarin doka da ake tafiya a kanta bisa wannan shari'a. Sakamakon haka ya bayar da belin Aisha a kan Naira dubu dari biyar, kuma dole mai karbar beli ya zama mai mutunci, kuma ya kasance yana da kadara a cikin garin Birnin kebbi. Daga bisani ya dage zaman Kotu har zuwa ranar 26 ga watan Satumba 2019 domin ci gaba da shari'a.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post