Birnin kebbi: Yadda samari suka yi zanga-zanga kan yawan matsalar wutan lantarki (Bidiyo)

Da safiyar Litinin wasu matasa da samari sun gudanar da zanga-zanga kan abin da suka alakanta da rashin wadataccen wutan lantarki da ruwan sha a garin Birnin kebbi.

Zanga-zangar ta taso daga titin Ahmadu Bello da ke garin Birnin kebbi zuwa gidan Gwamnatin jihar Kebbi, daga bisani suka juyo zuwa gidan Mai martaba Sarkin Gwandu.

Masuzanga-zanga, samari ne da yara kanana, wadanda suka yi ta ihu suna la'antar mahukunta da kanpanin ba da wutan lantarki.

Da farko dai zanga-zangar ta faro cikin lumana, amma bayan da masu zanga-zanga sun je gidan Gwamnati amma aka shaida masu cewa Gwamna Atiku Bagudu baya gari, sai suka juyo.

Latsa kasa ka kalli bidiyo:
Duk da yake Mujallar isyaku.com ta jiyo wasu suna gargadin samarin cewa kada su taba kowa ko barnata dukiya, amma lamarin ya gamu da cikas bayan masu zanga-zangan sun isa Shataletalen babban Masallacin Juma'a na jihar Kebbi, sai wasu matasa suka fara yaga postoci da buge bugen karafan postan da ke cikin shataletalen.

Hakazalika masu zanga-zangan sun buge yawancin postocin Gwamnan jihar Kebbi da na yan siya da ke kan titi tsakanin shataletalen Masallacin Juma'a na jihar Kebbi zuwa Asibitin Sir Yahaya.

A shataletalen Sir Yahaya, masu zanga-zangan sun yaga tare da buge postocin yan siyasa da ke ciki, daga bisani suka zarce zuwa gidan Mai martaba Sarkin Gwandu, amma jam'an tsaro sun hana su shiga .

Daga nan sai masu zanga-zanga suka dawo shataletalen Asibin Sir Yahaya suka ja burki, wasu samari sun banka wa postan yan siyasa da aka cire daga gidan Sarki wutaa, daga nan ne jamai'an yansanda suka fara harba barkonon tsohuwa ta bayansu, lamari da ya sa ala tilas masu zanga-zanga suka ranta na kare, suka tarwatse nan take wuri ya cika da hayakin barkonon tsohuwa.

Bayan minti biyar da haba barkonon tsohuwa, sai yansanadan kwantara da tarzoma cikin motoci guda biyu suka isa shataletalen Sir Yahaya, kuma suka zarce zuwa cikin gari, daga nan sai ga motar jami'an soji suma suka iso suka fara kame-kame tare da jami'an yansanda shiyar runduna ta garin Birnin kebbi.

Mujallar isyaku.com ta gano mataimakin Kwamishinan yansanda da DPO na yansandan shiyar Birnin kebbi suna kai kawo domin tabbatar da tsaro a shataletalen Sir Yahaya inda zanga-zangan ta ja burki.

Saidai kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya shaida mana cewa rundunar yansandan jihar Kebbi ta kama mutum gama sha biyar (15) kawo yanzu, kuma suna sashen SCIID ana gudaanar da bincike.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post