Kotu ta kashe auren shekaru 8 saboda duka

Legit Hausa
A yau Talata ne wata kotu dake Kaduna ta kashe auren shekaru 8 tsakanin Rashida Yakubu da mijinta, Muhammad Yahaya, akan batiri.
Mai shari'ar, Murtala Nasir, ya kashe auren ne bayan kokarin da yayi kan magabatan ma'auratan su sasantasu.
"Tunda Yahaya ya kasa gabatar da shaidunsa don karyata abinda matarsa ta sanar, kotu zata yanke hukunci ne bisa ga abinda magabatan ma'auratan suka yarda," inji alkalin.
Tun farko dai dama mai karar, Rashida Yakubu ta roki kotu da ta karbar mata saki wajen maigidan nata, saboda batiri da kuma rashin kula.
"Mijina dama ya saba dukana. Ya taba korata kuma ya sayar da kaya na," cewarta.
A kokarin kare kansa, Yahaya ya musanta abinda matarsa ta sanarwa da mai shari'a.
Ya sanar da kotun cewa shi fa yana kaunar matarsa kuma ya bukaci alkalin da ya bashi lokaci don rokar gafararta.
DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post