An maka wani Farfesa kara kotu a sakamakon ya tilastawa dalibansa yin zindir a gaban aji

Legit Hausa
Wani Farfesa dake koyarwa a Jami’atul Azhar dake kasar Masar zai gurfana a gaban kotu sakamakon tursasa dalibansa suyi zindir a gaban ‘yan ajinsu.
Jaridar Egypt Today ta ruwaito cewa Farfesan yana fuskantar laifuka guda biyu ne da ake tuhumarsa da aikatawa wadanda suka hada da cin zarafi da kuma sabawa dokar sanya tufafi da jami’ar.
Mun samu labarin cewa a watan Afrilun 2019, Jami’atul Azhar da sallami Farfesan tsangyar ilimin maza, inda ta bayyana laifin nasa a matsayin abu wanda ya saba dokar jami’ar. A don haka ya zama wajibi a kore shi.
A wani faifan bidiyo dake yawo, ya nuna cewa Farfesan ya tilastawa dalibai biyu cire wandunansu a gaban ajin da yake cike da dalibai. Ba a son ransu bah aka suka cire wandunansun saboda ya talista su.
Bincike ya tabbatar mana cewa, farfesan ya lashi takobin kayar da daliban a jarabawa idan har suka bijirewa umarnin da ya basu na cire wando.
Egypt Today ta sanar damu cewa, a sakamakon ikirarin da farfesan yayi na cewa zai fadar da su a jarabawa idan har suka bijirewa umarninsa, shi ne dalilin da ya sa har yaran suka yadda suka kwabe wandunan nasu.
A wani labarin kuwa za ku ji cewa, fitaccen jarumin Kannywooddin nan mai suna Adam A. Zango ya fadi dalilin da ya sa ya fice daga masana’antar Kannywood domin ya bude ta shi.
Zango ya ce tsananin kyashi da hassada daga wurin abokan aikinsa ne ya sanya shi barin masana’antar inda ya kafa tasa mai suna Kaddywood.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post