Albashin shugabanni da 'yan majalisun dattijai da na wakilan tarayya


Legit Hausa

An dade ana tafka muhawarra kan albashi da allawus din 'yan majalisar Najeriya. Akwai rahotanni da dama da suka wallafa mabanbantan adadin kudin da 'yan majalisar ke dauka a duk shekara. Duk da haka, muhimman abu a nan shine korafin da ake yi na cewa 'yan majalisar Najeriya suna daga cikin wadanda ke karbar albashi mai yawa a duniya har ma fiye da wasu takwarorinsu na kasashen da suka cigaba.

A 2015, Quartz Africa ta rubuta wani rahoto da ya ce 'yan majalisar Najeriya suna daga cikin wadanda suka fi daukan albashi mafi tsoka a duniya kuma ta gabatar da alkalluma daga The Economist domin kare wannan ikirarin. A 2018, tsohon dan majalisa, Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana cewa dan majalisa na karbar N750,000 a matsayin albashi duk wata tare da naira miliyan 13.5 a matsayin allawus jimla ya kama naira miliyan 14.25 duk wata.

Shin nawa ne ainihin albashin dan majalisar Najeriya? Legit.ng ta yi bincike kan albashi da allawus din da 'yan majalisar Najeriya ke karba duk wata.

Shugaban Majalisar Dattawa

Kamar yadda wani takarda da 'Revenue Mobilisation, Allocation and Fiscal Commission' (RMAFC) ta wallafa a bpsr.gov, albashin shugaban majalisar dattawan Najeriya a shekara shine N8,694,848:75 (N8.69m) yayin da albashinsa na wata kuma N722,570:72 Ga kiddidigar albashin na shugaban majalisar dattawa da allawus dinsa kamar yadda RMAFC ta wallafa.

Mataimakin Shugaban Majalisa

Mataimakin shugaban majalisar dattawa albashinsa na shekara shine 8,082,083:65 (N8.0m) yayin da albashinsa na wata kuma N673,507:00.

Sauran Sanatoci

Albashi da allawus din sauran sanatoci na shekara guda kamar yadda RMAFC ta wallafa shi N12,766,320:00 (N12.7m). Albashi da allawus din su na wata kuma shine N1,063,860:00 (N1.06m).

Albashin Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya

Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya yana karbar 4,954,220:00 (N4.95m) duk shekara, a kowane wata kuma yana daukan N412,851:66 amma banda allawus. Albashin sauran 'Yan Majalisar Wakilan Tarayya Albashin sauran 'yan majalisar wakilai na tarayya a cewar RMAFC a shekara shine N9,529,038:06 (N9.5m) yayin da albashnsu na wata kuma shine N794,086:83.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
 • Previous Post Next Post

  Reported by ISYAKU.COM

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp 
  https://chat.whatsapp.com/L2WpsKOTg5Q6ieoYKEWxeB

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu 
  LATSA NAN 

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA 

  Facebook.com/isyakulabari