Yadda wani bawan Allah ya shafe shekaru 36 a gidan kurkuku, saboda ya saci N18,000


Legit Hausa

An yanke hukuncin sakin wani mutumi daga gidan yari bayan ya shafe shekaru 36 a gidan yari saboda ya saci naira dubu goma sha takwas (N18,000). Mutumin mai suna Alvin Kennard an yanke masa hukuncin kisa ne ba tare da beli ba, a lokacin tsohuwar dokar Alabama.

An kama Kennard yaje yin fashi da makami a wani gidan biredi, inda ya saci dala hamsin ($50), kimanin naira dubu goma sha takwas. Tun lokacin mutumin mai shekaru 58 yake zaune a gidan kurkuku a matsayin hukuncin kisa.

Sai dai kwatsam kuma wani alkali ya karbi rokon da yake yi masa inda ya bayar da umarnin a sake shi. Yanzu haka dai alkalin kotun ya bayyana cewa yana cika wasu takardu ne domin aikawa gaba akan sakin Kennard.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post