Matsalar tsaro: Shehu Sani ya bayyana hanyar samun mafita ga gwamnonin Arewa


Legit Hausa

Tsohon dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani ya bayyana wata hanya daya kwakkwara da yake ganin idan har aka bi ta za’a samu saukin matsalar tsaro da ake fama dashi a yankin Arewacin Najeriya.

Legit.ng ta ruwaito Shehu ya bayyana haka ne a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook, inda yace da gwamnonin jahohin Arewa yake, walau su karbi shawarsa ko su yi watsi dashi, amma akwai bukatar gwamnonin su tattaro kwararru a harkar tsaro don ceto yankin.

“Idan har ana son kawo karshen matsalar tsaro a Arewacin Najeriya, ya kamata gwamnonin Arewa su kafa wata kwamiti da zai kunshi mutane kamarsu Janar Aliyu Gusau, Janar Magoro, Janar Agwai, Janar Buba Marwa, Kanal Umar, Kanar Gwadabe.

“Da sauran tsofaffin sufetan Yansandan Najeriya da suka fito daga yankin Arewa, da kuma tsofaffin jami’an tsaron farin kaya dana sirri yan asalin yankin Arewa domin su zauna tare su tattauna matsalar tare da samar da hanya daya wanda za’a bi, su fidda rahoto.

“Kuma gwamnonin su tabbata sun aiwatar da rahoton wannan kwamiti domin taimaka ma kokarin da gwamnatin tarayya ke yi don magance matsalar kashe kashe da garkuwa da mutane a yankin.

” Inji shi. A wani labarin kuma, a sakamakon tabarbarewar tsaro a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja, musamman a cikin makonnan inda yan bindiga suka ci karensu babu babbaka, babban sufetan Yansandan Najeriya ta sake shirin yaki da miyagun.

A yau ne babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Adamu ya aika da tawagar yansanda ta musamman dake kai agajin gaggawa, IRT, zuwa hanyar Kaduna-Abuja a karkashin jagorancin jarumin Dansanda, DCP Abba Kyari don tabbatar da tsaro a kan hanyar.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post