Yan bindiga sun kashe mutane 5, sannan sun kona gidaje da dama a Kaura jihar Kaduna


Legit Hausa

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane biyar ne suka mutu yayinda aka kona wasu gidaje da dama, a wani hari da wasu yan bindiga suka kai kauyen Zangan da ke Takad a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Mista Bege Katuka, Shugaban rikon kwarya na karamar hukumar wanda ya tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta, yace maharan sun kai mamaya kauyen da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Alhamis, sannan suka yi ta harbi ba kakkautawa akan bayin Allah.

 “An kashe mutane biyar yayinda har yanzu ba a ga wasu biyu ba. An kuma kona wasu gidaje da dama. “Mun bukaci mutane da su kwantar da hankalinsu sannan su yi imani da jami’an tsaro da suka riga suka yi wa yankin kawanya yayinda ake ci gaba da gudanar da bincike,” inji shi.

Jaridar Daily Trust cewa kauyen Zangan inda mummunan al’amarin ya afku, na raba iyaka da karamar hukumar Riyom da ke jihar Plateau. A halin da ake ciki, duk wani kokari da ake don tabbatar da lamarin daga kakakin yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ya ci tura domin bai amsa kiran waya da sakon da aka tura masa ba.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post