Yadda Iran tayi amfani da kudi wajen jan ra'ayin dan uwa na - Yayan Zakzaky


Legit Hausa

Sheikh Mohammed Yakoob, dan uwan shugban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya yi fashin bakin kan rayuwan shugaban na 'Yan Shi'a tun yana kuruciyya zuwa girmansa musamman yadda Iran tayi amfani da kudi don sauya tunaninsa ya shiga Shi'a.

Ted Odugwu ya yi hira da Sheikh Yakoob na a filin tashi da sauran jirage na Aminu Kano a hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don sauke farali a bana. Ya ce El-Zakzaky mutum ne da ke da baiwar haddace karatu ta sauran fahimtar duk abinda ya karanta tun lokacin da suke makarantar frimare. Yakoob ya ce, "Bayan mun kammala firmare.

El-Zakzaky ya tafi Kwallejin Horasa da Malamai na Kano (FCE Kano) yayin ni kuma ta nafi Kwallejin Horas da Malamai ta Katsina. A lokacin ne ya kulla alaka da Iran amma bai zaman dan Shi'a ba. "Amma bayan ya kammala karatun digiri daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya fara tara dalibai yana musu wa'azin addinin musulunci.

Ya koyo wannan salon ne daga Iran kuma ya fara samun kudi. Iran ta gayyaci shi zuwa kasar domin ya shiga Shi'a sannan su fara bashi kudin tallafi. Da farko El-Zakzaky sunni ne amma Iran tayi amfani da kudi wurin sauya tunaninsa. "El-Zakzaky ya zama dan Shi'a ne bayan ya ziyarci Iran inda suka masa alkawarin nada shi wakilin Shi'a a Najeriya.

Ya canja sosai musamman saboda kudin da ya ke samu daga Iran." Shiekh Yakoob ya kara da cewa baya tare da dan uwansa saboda akidarsa ta Shi'a ba su son zaman lafiya da girmama dokokin kasa hakan yasa 'yan Shi'an suka kaiwa Hafsan Sojojin Kasa ta Najeriya, Laftanat Tukur Buratai hari inda suka hana shi wucewa domin hallartar taro a Zaria. Ya kuma ce 'Yan Shi'a ne umml abba'isin fitintunin da ake fama da su a yankunan gabas ta tsakiya musamman kasashen Iraqi, Yemen da Syri'a.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post