Tsohuwa fitacciyar fim fin Indiya ta kashe diyarta budurwa, ta kashe kan ta

Legit Hausa
Toshuwar jarumar fina-finan kasar Indiya, Pradnya Parkar, mai shekaru 40 ta kashe diyarta budurwa kafin daga bisani ta kashe kan ta.
Parkar ta kashe matashiyar diyarta ne ta hanyar shake mata wuya a gidansu dake unguwar Kalwa a yankin Gauri Suman, kamar yadda 'yan sanda a Thane suka sanar ranar jama'a da safe.
Tsohuwar jarumar ta bar wasika kafin mutuwar ta inda ta amsa cewa ita ta kashe diyarta, Shruti, mai shekaru 17, daliba a makarantar sakandire dake Thane.
A cikin wasikar, jarumar ta bayyana cewa tana cikin damuwa mai tsanani.
Sakamakon bincike na farko-farko da jami'an 'yan sanda suka sanar ya nuna cewa Parkar ta dade a gida ba tare da samun gayyata domin fito wa a wani shirin fim ba. Kazalika, mijinta ma yana fuskantar kalubale a cikin harkokin kasuwancinsa.
Wani babban jami'in dan sanda a ofishin Kalwa, Shekhar Bagde, ya bayyana cewa daga cikin damuwar marigayiyar akwai batun cewa ta gano mijinta na mu'amala da mata a waje.
Parkar ta kashe diyarta da kan ta ne da misalin karfe 8 zuwa 9 na safe lokacin da mijinta ya fita motsa jiki.
Sai da makwabta suka taimaka wa mijin aka balle kofar gidan da marigayiyar ta rufe kafin ta aikata kisan da ta yi.
"Ta bar takardar cewa ita ce ta aika kisan, kuma kar a zargi kowa. Anna muna tunanin cewa matsalolin kudi ne silar damuwar ta," a cewar Badge.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post