Yanzu Yanzu: Adam A. Zango ya yi hadarin mota a Nijar


Legit Hausa

Shahararren jarumin Kannywood kuma mawaki, Adam A. Zango ya yi hatsarin mota a kan hanyarsa ta dawowa daga Jamhuriyar Nijar tare da wasu abokansa kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Instagram.

Amma jarumin ya ce babu abinda ya same su sai dai motarsu ce hatsarin ya yi wa illa kamar yadda BBC ta ruwaito Zango yana yawan yin balaguro musamman lokutan bukukuwa ko shagali kamar na sallah babba da karama saboda gayyatarsa da ake yi domin yin casu. Duk kokarin da BBC tayi don ji ta bakinsa kan lamarin bai yi wu ba kawo yanzu saboda bai amsa wayarsa ba.

Sai dai bayyanai a shafinsa na Instagram sun nuna cewa jarumin ya tafi Niyami, babban binrin Nijar ne don yin wasan sallah. Galibi dai a kan samu yawaitan hadurra a hanyoyin Najeriya musamman lokutan bukukuwa kamar Sallah, Kirsimeti da bikin sabuwar shekara. Masu nazarin al'amura su kan daganta hakan da rashin kyawun tituna da kuma tukin ganganci daga bangaren direbobi.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post