kiki-kaka kan likitoci: Elzakzaky zai dawo Najeriya ba tare da an duba lafiyarsa ba


Legit Hausa

Shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), wacce aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, na a hanyarsa na dawowa Najeriya daga asibitin Indiya inda ya je yin magani. Kakakin kungiyar ta IMN, Ibrahim Musa, ya tabbatar wa manema labarai cewa shugaban na Shi’a zai dawo Abuja da karfe 5:00 na yamma.

Har ila yau, a cewar wani rubutu da aka wallafa a shafin Twitter daga ofishin Zakzaky, ana sanya ran shugaban kungiyar na IMN zai iso Abuja da karfe 17:00. Wani bidiyo da aka wallafa tare a shafin Twitter ya kuma nuno El-Zakzaky yana bayanin cewa asibitin Indiya ta amince za ta bari ya dawo Najeriya tare da matarsa Zeenat, biyo bayan rikicin da ya barke kan zabi na likitocin da za su kula da su da kuma ka’idojin jinyan.

Malamin ya bayyana cewa mahukuntan yankin da ya je neman magani a Indiya sun gaya masa cewa sun yanke hukuncin mayar da shi Najeriya. Idan za ku tuna dai tun bayan isarsa kasar ta Indiya a ranar Talata aka samu kiki-kaka kan likitocin da za su duba shi da mai dakinsa, inda ya yi zargin cewa "an sauya masa likitocin da ya zaba tun farko, yana mai cewa ana tsare da shi cikin mummunan yanayi".

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta kalaman nasa, tana mai cewa ya yi kokarin bijirewa sharudan da kotu ta gindaya masa, sannan ta bai wa gwamnatin Indiya hakuri kan mummunar halayyar da ya nuna.
 

DAGA ISYAKU.COM 

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post