Rayuwa mai albarka: Dattijon da ya rubuta Al-Qur'ani sau 70 da hannayensa


Legit Hausa

Alhaji Shu'aibu Sa'eed Usman mutumin arewacin Najeriya ne, wanda yake da kimanin shekaru 80 a duniya. An tabbatar da cewa ya rubuta Al-Qur'ani daga Bakara zuwa Nasi sau 70 a rayuwarsa. An ruwaito cewa akwai lokacin da ya taba rubuta AL-Qur'ani izu sittin a cikin kwana 60 kacal. Wannan shine mafi karancin lokacin da ya taba dauka yana rubutun Al-Qur'ani mai girma.

Alhaji Shu'aibu da iyalinsa suna zaune a wani karamin dakin soro. Kullum wuni yake yi cikin tilawa da rubuta Al-Qur'ani a daki daya, sannan da dare sai ya kwana a daya dakin. Labarin wannan bawan Allah ya yadu a kasashen Larabawa shafukan sada zumunta da kuma dandalin ajiye bidiyo na Youtube. Sannan akwai lokacin da wani Balarabe ya ziyarce shi har gidansa yayi hira dashi.

Larabawa sun yi mamakin samun irin wannan mutumi mai baiwa haka duk kuwa da kasancewarsa a cikin talauci. Alhaji Shu'aibu kwararrene a fannin Al-Qur'ani ya san adadin kowacce kalma da kuma wuraren da suke a cikin Al-Qur'ani, sannan kuma nan take idan ka tambayeshi zai fada maka sannan yayi bayani daga inda kalmar ta fara zuwa inda ta tsaya.
 

DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post