Rundunar soji ta kaddamar da wasu sabbin motoccin yaki 4 da aka kera a Najeriya (Hotuna)

Legit Hausa
Rundunar Sojojin Najeriya ta kaddamar da sabbbin motoccin yaki wadanda nakiya baya fasa su guda hudu da aka kera a Najeriya da hadin gwiwar Proforce Limited domin taimakawa sojoji yaki da ta'addanci.
Shugaban hafsin sojojin kasar Najeriya Laftanat Janar Tukur Buratai yana daya daga cikin manyan bakin da suka hallarci taron kaddamar da sabbin motocin yakin.
Proforce Limited kamfanin Najeriya ne da ya kware wajen kerawa da inganta motocin yaki iri daban-daban har da wadanda nakiya ba ta iya fasa su.
An rada wa motar sunan 'Thunder' wadda ke nufin tsawa saboda ingancin ta ba karko musamman a filin daga. An fara kadamar da motar ne a shekarar 2017 amma daga bisani aka sake komawa domin inganta tsarin.
An kaddamar da sabbin motocin yaki wadanda nakiya bai iya tarwatsa su
Babban hafsin sojojin kasan Najeriya, Laftanat Janar Tukur Buratai da manyan baki yayin kaddamar da sabbin motoccin yaki
An kaddamar da sabbin motocin yaki wadanda nakiya bai iya tarwatsa su
Sabbin motoccin yaki na musamman da aka kera wa sojojin Najeriya
An kaddamar da sabbin motocin yaki wadanda nakiya bai iya tarwatsa su
Laftanat Janar TY Buratai yayin da ya ke dubba sabbin motocin yaki
An kaddamar da sabbin motocin yaki wadanda nakiya bai iya tarwatsa su
Laftanat Janar TY Buratai ya duba sabbin motoccin yakin sojojin Najeriya
An fara aikin inganta motocin yakin ne saboda halin da sojojin Najeriya ke ciki ne yaki da 'yan ta'addan da suke adabar wasu sassa na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sojojin Najeriya sun kwashe kimanin shekaru bakwai suna fafatawa da 'yan ta'addan hakan ya sa su kayi shawarar canja salo da dabarun yaki daga amfani da tsohuwar motar Toyota zuwa sabbin motoccin yaki daga kasashen waje. Hakan ya sa aka fara kera motocin a gida Najeriya.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post