An yiwa wata budurwa bulala 100 a bainar jama'a bayan an kama ta da laifin aikata zina da wani saurayinta


Legit Hausa

Wata mata ta koka inda ta bukaci wani mutumi da yake yi mata bulala da ya daina dukanta, a lokacin da ake yiwa masu laifi irin nata bulala ranar Larabar nan da taa gabata a kasar Indonisiya. Matar mai shekaru 22, wacce aka yi mata hukunci akan laifin da ta yi na zina, tana daya daga cikin mutane ukun da aka yiwa bulala dari a ranar.

Mutane masu dumbin yawa suna kallo a lokacin da ake yiwa mazan guda biyu da mace daya bulala a filin wasa na Lhokseumawe,. Bulala ana yinta ne a matsayin hukunci ga wasu laifuka da suka hada da caca, shan giya, luwadi da kuma zina ba tare da aure ba a yankin tsibirin SUmatra.

Ranar Larabar budurwar da saurayinta an yi musu bulala dari-dari, inda budurwar ta ta dinga faduwa saboda zafin bulalar. Haka shima wani saurayi dan shekara 19 wanda aka kama shi da laifin zina, an yi masa bulalar inda har rigar shi ta jike da jini.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post