Kawaye uku sun hada kai sun yiwa saurayinsu dukan tsiya bayan sun gano yana soyayya dasu uku a boye

Legit Hausa
Wani mutumi dan kasar Kamaru ya gamu da gamonsa, bayan 'yan mata guda uku wadanda suke aminan juna sun yi masa dukan tsiya yayin da suka gano cewa yana wasa da hankalinsu wajen soyayya da su duka a boye.
Wannan dalilin ne yasa 'yan matan suka zauna suka shirya yadda za su kawo karshen lamarin, inda suka hada kai suka tunkari mutumin suka yi masa dukan tsiya, sannan suka gargadeshi akan kada ya kara shiga harkar su.
Wannan lamari da ya faru a kasar ta Kamaru ya jawo hankalin mutane da yawan gaske a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da Instagram, inda wasu ke ganin hukuncin da 'yan matan suka dauka bai kamata ba.
Wasu kuwa musamman mata da suka saba da irin wannan rainin wayo na samari sun bayyana cewa abinda 'yan matan suka yi daidai ne domin kuwa da yawa sun nuna idan sune a irin wannan halin irin wannan hukuncin zasu dauka.
Allah dai ya kyauta, ya kuma raba mu da yaudara.
DAGA ISYAKU.COM
Previous Post Next Post