Kaico: Wuta ta babbake wata budurwa mai bunburutun man fetur

Legit Hausa
Wata budurwa mai shekaru 20, Mary Agada da ke sana'ar bunburutu ta mutu sakamakon konewa da tayi kurmus.
Lamarin ya faru ne a garin Igbogor da ke karamar hukumar Ovia South West a jihar Edo.
Rahotanni sun bayyana cewa marigayiyar tana sayar da man fetur ne a galan a garin.
Mutane sun bayar da mabanbantan bayanai kan yadda gobarar ta fara.
Wasu da abin ya faru a idanunsu sun ce gobarar ta fara ne yayin da marigayiyar ke kokarin kuna risho domin dafa abinci.
A cewar wani ganau, ta ajiye man fetur din ne a kitchin din ta kuma tana zubuwa wani kostoma man fetur ne lokacin da gobarar ya fara ci daga wutar da ta kunna a risho.
Mijinta, Mr Amend Agada ya sha da kyar duba da cewa yana tare da ita a cikin kitchin din lokacin da gobarar ta fara.
An ruwaito cewar ya daka tsalle ya fito waje amma matarsa ta riga ta kama da wuta.
Shaidun ido sun ce mijin ya yi yunkurin ceto matarsa amma hakan bai yi wu saboda wutar da ke ci hakan nan ya zuba idanu har matarsa ta kone.
Tuni an tafi da gawarta zuwa jihar Benue domin yi mata jana'iza.
Mai magana da yawun 'Yan sandan jihar, DSP Chidi Nwabuzor ya ce har yanzu ba a sanar da su afkuwar lamarin ba.
DAGA ISYAKU.COM
Previous Post Next Post