Hawan jini a shekarun kuruciya ka iya janyo dimaucewa

BBC Hausa
Ya kamata masu shekaru 30 da 'yan kai su rinka sa ido kan yanayin hawa da saukar jininsu domin riga-kafi daga matsalar kwakwalwa da ka iya samun mutum idan ya manyanta, kamar dai yadda wani nazari ya nuna.
Nazarin dai ya duba yanayin mutum 500 da aka haifa a shekarar 1946, inda ya alakanta hawan jini a shekarun kuruciya da samun matsalar kwakwalwa a lokacin girma.
Kwararru sun ce hawan jini a lokacin da mutum yake ganiyarsa a shekaru 30 zuwa 40 na janyo samun matsala a tunanin mutum sakamakon taba kwakwalwa da yake yi.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake alakanta hawan jini da a shekarun ganiya da matsalar mantuwa ko kuma dimaucewa ba, To sai dai masana ilimin kimiyya sun zaku su san yaushe ne da kuma ta yaya hakan ke faruwa a rayuwa.
A cikin wannan nazarin, wanda aka buga a mujallar Lancet Neurology, wadanda aka tattauna da su an gwada hawan jininsu sannan an dauki hoton kwakwalwarsu.
A nan aka gano cewa samun hawan jini a shekaru 36 zuwa 43 ka iya samun alaka da kankancewar kwakwalwa.

Kankancewar kwakwalwa

Abu ne da aka sani cewa kowa kwakwalwarsa na kankancewa saboda shekaru, to sai dai an fi samun matsalar kankancewar ne ga wadanda suke da rashin lafiyar kwakwalwar kamar masu cutar dimauta.
Duk da cewa nazarin bai fito da wasu alamu na dimaucewa ba, masu nazarin sun ce kankancewar kwakwalwa ce ke haddasa dimaucewa.
Yanzu haka masanan za su ci gaba da sa ido a kan mutanen da ake nazarin a kansu domin ganin ko za a samu alamun dimaucewa a rayuwarsu nan gaba.
Artist's image of memory lossHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionMutum mai hawan jini yana ganiyarsa na samun matsalar kwakwalwa idan ya girma
An kuma alakanta hawan jini a tsakanin shekaru 43 da 53 da alamun lalacewar jijiyoyin jini ko kuma bugun jini a lokacin da mutum ya kai shekara 70.
Farfesa Jonathan Schott, kwararre a kan kwakwalwa a Cibiyar Nazarin Cututtukan Kwakwalwa ta UCL Queen Square Institute of Neurology ne ya jagoranci nazarin.
Ya ce "Hawan jini ko da a shekara 30 da doriya ka iya haddasa wa kwakwalwa matsala a shekaru 40 masu zuwa. Saboda haka kula da ingancin kwakwalwa ya kamata ya fara daga shekarun kuruciya ne."
Paul Leeson, wanda shi kuma farfesa ne na abin da ya shafi zuciya a jami'ar Oxford, ya ce, "Mun gano cewa akwai yiwuwar masu hawan jini ka iya samun matsalar kwakwalwa a lokacin da suka manyanta.
"Abin da likitoci suka dade suna muhawara a kai shi ne ko magance hawan jini ga masu karancin shekaru na maganin kamuwa da matsalar kwakwalwar."
Dr Carol Routledge, darakta a cibiyar nazari ta Alzheimer's Research da ke Burtaniya, ta ce, "Hawan jini a matsakaitan shekaru na cikin abubuwan da ke haddasa cutar dimuwa a lokacin girma, wani al'amari da lura da shi ke hannunmu.
"Bincike ya nuna cewa hanya sahihiya ta magance hawan jini ita ce inganta lafiyar kwakwalwar matasan yanzu wadanda su ne dattijan gobe."

DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN