Mai yiwuwa ne talakawa su yi wa masu kudi bore idan basu gyara halinsu ba- Melaye

Legit Hausa
Fitaccen Sanatan na Najeriya watau Dino Melaye ya gargadi Mala’un Najeriya su bi a hankali da dabi’unsu inda ya ce nan gaba Talakawan da ke cikin al’umma za su tashi su juya masu baya.
Sanatan na PDP ya hango cewa wata rana za a yi wa Attajiran kasar nan bore idan har ba su taimakawa Talakawa. Dino Melaye ya ce zai zo su kansu masu kudin ba za su iya more dukiyarsu ba.
‘Dan majalisar mai wakiltar Yammacin jihar Kogi ya yi wannan jawabi ne a wani bidiyo da ya saka a shafinsa na Tuwita. Gawurtaccen ‘Dan siyasar ya yi kira ga gwamnati ta ba matasa hanyar samu.
Ga dai abin da Sanatan na PDP ya ke fada da bakinsa: “Dole gwamnatin mu ta kirkiro hanyar da Matasan kasar za su samu na kan su. Kowace kasa a Duniya ta na samun shugaban kasa ne daidai da ita.
Melaye ya cigaba da cewa: “Mala’un Najeriya ba su ka kai 5% ba. Bai kamata a kyale kashi 5% su matsawa kashi 95% na al’umma ba. Manyan kasa wanda ina cikinsu, ba su da wani karfi a karan kansu.”
“…Abin da mu ke yi shi ne mu yi amfani da karfin ofishin mu, mu rika gallazawa Talaka. Shi Talaka bai san jama’a ne ke da ainihin karfi ba kuma za su iya sanya manya su yi masu abin da su ke so.”
Mai neman takarar gwamnan na Kogi ya kara da ja kunne da gargadi cewa: "Idan masu kudi ba su yi abin da ya kamata ba, a karshe Talakawa za su cinye su a danyensu idan su ka rasa abin da za su ci."
“Za a zo lokacin da Attajirai ba za su iya hawa wadannan manyan motoci a kan titi ba, bari ma har an fara zuwa wannan lokaci. Yanzu an soma satar mutane a na garkuwa da su, wanda a da ba ayin haka”
Fitaccen ‘dan siyasar kasar ya ce dole yanzu masu kudi su rika boye kansu, kuma ya ce idan Talaka ya gaji, zai dura kansu, muddin ba a samu hanyar da za a rika taimaka masa a cikin al’umma ba.

DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN