Da duminsa: Gwamna Wike ya yi magana a kan rushe Masallacin Juma'a a Ribas

Legit Hausa
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi Alla-wadai da labaran karyar da ake yada wa a wasu kafafen yada labarai da dandalin sada zumunta a kan cewa gwamnatin jiharsa ta rushe wani Masallaci a garin Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Wike ya bayyana masu yada labarin a matsayin makiya jihar Ribas da ke burin son haddasa fitina a tsakanin al'umma.
Da yake ganawa da manema labarai a kan titin Biambo dake kusa da kwanar tsohuwar kasuwar Mami, wurin da aka ce an rushe masallacin, Wike ya ce babu wani ginin Masallaci a wurin, a saboda haka ba a rushe wani gini ba a wurin.
"Manyan mutane a fadin kasar nan sun kira ni a kan labarin rushe Masallaci a Fatakwal da ke yawo a yanar gizo. Shi yasa na zo har wurin da 'yan jarida domin su ga wurin, su san cewa babu wani Masallaci a wurin.
"Abin bakin ciki ne a ce wasu mutane, da babu alheri a cikin zuciyarsu, suna yada cewa an rushe Masallaci a wannan wurin, yayin da babu wani gini ma a wurin. Wasu makiya jihar Ribas ne ke yada labarin domin cimma muguwar manufarsu," a cewar Wike.
Gwamna Wike ya bayyana cewa gwamnati ta sa an baje wurin ne bayan wasu mutane sun fara gini ba tare da izini ba a wurin.
"Sun zo sun fara gini ba tare da samun sahalewar hukuma ba. Gwamnatin jihar Ribas ba ta bawa kowa izinin yin ginin a wurin ba.
"Mutanen da suka zo suka fara gini a wannan wuri tuni suka garzaya kotu a kan magabar filin wurin, kuma gwamnatin jihar Ribas ce ta samu nasara a kotu. Amma duk da haka suka fara gini a wurin domin kawai su jazawa gwamnatin jihar Ribas bakin jini," a cewarsa.
Gwamnan ya kalubalanci Musulman jihar Ribas da su nuna wurin da gwamnati ta rushe musu Masallaci tare da basu shawarar cewa kar su bari a yi amfani da su domin dalilan siyasa.
DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post