Fusataccen miji ya kashe surukin wanda ke neman matarsa, ya kone gidaje biyu

Legit Hausa
Wani fusataccen magidanci ya kashe surukin kaninsa a yankin Amukpe da ke Sapele a jihar Delta bayan ya gano cewar kanin nasa da suka fita ciki daya ya na cin amanarsa tare matarsa.
Majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewa magidancin, wanda ba a bayyana sunansa ba ya zuwa yanzu, ya tsere bayan ya harbe surukin kaninsa.
Kazalika, lamarin ya yi sanadiyyar kona gidaje guda biyu; daya na mutumin da magidancin ya kashe, daya kuma na kaninsa, wanda aka bayyana cewa sunansa Pius.
A cewar wata majiyar, matar magidancin ce ta sanar da shi cewa ita da kaninsa, Pius, suna kwana tare.
Shi kuma magidancin ya dauki bindiga cikin fushi ya nufi gidan surukin kanin nasa, inda bayan cacar baki ya harbe shi.
Rahotanni sun bayyana cewa margayin ya kalubalanci fusataccen magidanci a kan ya harbe shi idan ya isa, lamarin da ya sa shi kuma ya harbe shi a ido, inda nan take ya fadi ba tare da ko shura wa ba.
Majiyar mu ta bayyana cewa 'yan uwan mutumin da aka kashe ne suka kone gidan Pius saboda jin haushin kisan dan uwansu.
Wani shaidar gani da ido ya ce lamarin zai fi haka kazanta ba don jami'an tsaro sun shiga tsakani ba.
Kazalika, hedikwatar rundunar 'yan sanda a jihar Delta ta tabbatar da faruwar lamarin, tare da bayyana cewa sun shiga farautar fusataccen magidancin.
A hira da aka yi da shi ta wayar tarho, kwamishinan 'yan sandan jihar Delta, Adeyinka Adeleke, ya ce, "na samu labarin wani mutum da ya kashe surukinsa a Amukpe, Sapele, saboda matarsa na kwanciya da kaninsa. An kone gidaje guda biyu; na mutumin da aka kashe da kuma kanin magidancin da ya aikata kisan, wanda kuma shine ke lalata da matar yayansa. Ya gudu, amma mun shiga nemansa."h
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post