Abba Vs Ganduje: PDP ta gamu da babban cikas, kotu ta yi watsi da wasu shaidu 68


Legit Hausa

A ranar Talata ne jam'iyyar PDP ta gamu da cikas a kotun sauraron korafin zaben gwamnan jihar Kano, bayan kotun ta yi watsi da bukatar jam'iyyar na neman a bata izinin kara yawan shaidun da zasu bayar da shaida a gaban kotun.

Adegboyega Awomolo (SAN), lauyan masu kara, ne ya nemi kotun ta basu damar daidaita sunayen shaidunsu da haruffan da aka yi amfani da su wajen sakaya sunayen shaidu tare da sake neman kotu ta basu izinin sake yiwa jerin shaidun kwaskwarima.

A cikin wata takarda da ya gabatar a gaban kotun amadadin jam'iyyar PDP da dan takarar ta na gwamna a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a ranar 31 ga watan Yuli, 2019, Awomolo ya roki kotun ta basu damar sake duba sunayen shaidun da suka bayar domin daidaita su da haruffan farko na sunayensu na gaskiya.

Sai dai, Offiong Offiong (SAN), lauyan da ke kare gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya kalubalanci wannan bukata ta masu kara tare da bayyana cewa suna son sake cusa sunayen wasu shaidun ne da basu bayar da sunansu tun farko ba.

Kazalika, shi ma lauyan jam'iyyar APC, Barista Alex Iziyon, ya goyi bayan lauyan Ganduje wajen kin amincewa da bawa PDP da Abba damar yin wani gyara ko kwaskwarima a sunayen shaidun da suka fara gabatar wa a gaban kotun. Kotun, karkashin jagorancin Jastis Halima Shamaki, ta yanke hukuncin cewa ba zata bawa PDP da Abba damar taba sunan shaidunsu ba saboda suna niyyar cusa sunayen wasu sabbin shaidun.

Shamaki ta bayyana cewa shari'ar korafin zabe na da takaitaccen lokaci kuma lokacin saka sunan sabbin shaidu ya wuce. Kotun, mai alkalai guda uku, ta bayyana cewa duk wani yunkuri na sake shigar da sunayen shaidu, tamkar yunkurin keta haddin kotun ne.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post