Awa 6 da fara aiki,mai aikin gida ta sace naira miliyan 1.6 a gidan

Wata budurwa mai suna Franca Amaha ta fada hannun yansandan jihar Lagos bayan ta sace Naira miliyan daya da dubu dari shida a gidan da aka dauketa aikin gida awa shida bayan ta fara wannan aiki a gidan da ke Surulere.

Bayan an dauki Amaha aikin gida bisa albashin N20.000 kowane wata ta hannun ajent, ashe Amaha ta bayar da suna da adireshin bogi ne a takardu da ta cika a wajen ajent ranar 24 ga watan Yuli 2019.

Amma bayan an hada ta da sabuwar uwargida da zata dinga aiki a gidanta, a ranar farko na kama aiki a gidan, sai yar uwar uwargidanta ta dawo daga Turai, kuma aka tafi tare da Amaha aka dauko ta a filin saukan jiragen sama na IKeja a birnin Lagos.

Amma bayan sun iso gida, sai Amaha ta shiga dakin da aka ajiye kayan yar uwar uwargidanta ta bude Jaka ta dauke Daloli da kudaden kasar waje da matar ta zo da su da aka kiyasta su a darajan Naira miliyan daya da dubu dari shida kuma ta gudu.

Daga bisani dai ta kashe wayoyinta kuma ta boye, amma jami'an yansanda sun gano ta a gidan wata kawarta a birnin Lagos.
 
DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

 https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post