Yadda aka tilasta wata mata yin rantsuwa a kan wata gawa

Allah daya gari banban, an tilasta wata mata ta rantse a kan wata gawa cewa ba ita ta kashe gawar ba. Wanna lamari ya faru ne a garin Ibeku na jihar Abia.

Tun farko dai wannan gawar budurwa ce makwabciyar matar da aka fi sani da suna Mama thankgod, sai kawai aka ga wannan budurwar ta yanke jiki ta fadi ta mutu.

Sakamakon haka yanuwanta suka tilasta Mama thankgod cewa ala tilas ta rantse da wanan gawar kafin a binneta, kuma matar ta aikata abin da aka umurceta ta yi na rantsuwa a kan gawar.

A cewar su idan ba abin da ya faru da Mama thankgod  har zuwa kwana bakwai tau lalle ba ta da hannu a kashe budurwar. Amma yanuwan budurwar sun ce wa'adin lokacin da Mama thankgod za ta shafe shine wata shida bisa al'adar garinsu sannan idan ba abin da ya faru da ita, to bata da hannu a kshe yar uwar su.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post