An kama masu bautar kasa 6 na bogi a wata jihar arewa


Legit Hausa

Mun samu cewa a ranar Asabar wasu masu yi wa kasa hidima shida na boge sun shiga hannu a sansanin masu bautar kasa NYSC da ke jihar Katsina kwanaki kadan bayan da aka fara zaman sansanin na makonni uku. Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, shugaban hukumar NYSC na jihar, Alhaji Ahidjo Yahaya, shi ne ya bayar da shaidar hakan a wata hira da manema labarai yayin gabatar da wasu 'yan bautar kasa biyu mata na bogi da aka cafke.

Biyo bayan wani bincike da babban shugaban hukumar NYSC na kasa, Birgediya Janar Shu'aibu Ibrahim ya jagoranta, an samu nasarar cafke 'yan bautar biyu da takardun kammala karatun digiri na boge, wanda suka amsa laifinsu babu wata-wata inji Alhaji Yahaya.

Masu bautar kasar biyu na boge da aka gabatar wa manema labarai sun bayar da sunayensu tare da lambobin shaida kamar haka: Merienwa Chimdinma Ngozi (KT/19B/3836) - NYSC /ISU/2019/259331 daga jami'ar jihar Imo da kuma Offor Chinelo Blessing (KT/19B/3696) - NYSC /ISU/2019/260/22. Ana iya tuna cewa hukumar NYSC gabanin fara zaman sansanin wadanda suka kammala karatu a bana, ta yi gargadin cewa ba za ta sassauta wa duk wanda ta damka da takardun boge, lamarin da ta ce za ta mika shi ga hukumar 'yan sanda domin daukar mataki.

A wani rahoto mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohuwar ministar kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun, ta yi murabus daga kujerarta bayan an gano laifi da aikata na amfani da takardar shaidar hidimar kasa ta boge domin samun damar yin aiki a Najeriya.
 

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post