An gano gawar wata budurwa da aka yi wa fyade har ta mutu (Hotuna)An gano gawar wata budurwa tsirara a mace a bayan wani Chochi watau Mujami'ar Grace Tower Church da ke Nyiman a birnin Makurdi babban birnin jihar Benue da safiyar yau.
 
Mujallar isyaku.com ya tattaro cewa ana zargin cewa an yi wa budurwar fyade ne har rai ya yi halinsa kasancewa an sami tufafinta a gefen wajen da lamarin ya faru.

Saidai Kakakin yansandan jihar Benue ta tabbatar da mutuwar budurwar, amma ta musanta cewa an yi wa budurwar fyade ne har ta mutu, ta ce binciken Likita kan gawar ne kawai zai iya tabbatar da haka.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post