Abin mamaki: Yadda wata mata ta kama mijinta yana lalata da budurwarsa a cikin mota

Wata mata ta cika da mamaki da bakin ciki ganin yadda Allah ya tona asirin mijinta yayin da yake lalata da budurwarsa a cikin motarsa. Duk da yake wannan mata ta kama shi turmi tabarya tare da wannan budurwa, amma fa ko a jikinsa.

Mujallar isyaku.com ya tattaro cewa matar ta ce " Na tafi wajen daurin aure tare da mijina a cikin motarsa inda ya sauke ni shi ma ya sauka muka shiga wajen bikin daurin aure, amma da karfe shida na yamma sai na nemi mijina sama ko kasa ban ganshi ba.

Daga bisani na tafi Mujami'a bayan wani abokinsa ya rage mani hanya da motarsa, kai jama'a! gaskiya abin da na gani ya bani matukar tsoro da mamaki, domin dai bayan na zagaya wajen da ake aje motoci sai na gan mijina yana lalata tare da budurwarsa.

Ganin haka sai na kwankwasa gilashin tagar motar, sai ya daga kai ya kalle ni, daga bisani kuma sai kawai ya dauko rigarshi ya rufe fuskan budurwar shi kuma ya ci gaba da lalata abinshi. Ganin haka ya sa na sake nazari kan zamantakewarmu kuma ina neman shawara, wannan mijin aure ne ko kuwa mazinaci ne da kawai zan kashe aurensa ?".

DAGA ISYAKU.COM 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN


Previous Post Next Post