Tsegumi: Ali Nuhu zai zama ministan wasanni da matasa a gwamnatin Buhari


Legit Hausa

Wani labari da yake ta yawo a shafukan sada zumunta na zamani, irinsu Facebook, Twitter da Instagram, sun nuna cewa akwai yiwuwar fitaccen jarumin wasan Hausa na Kannywood din nan, Ali Nuhu, zai iya zama Ministan Wasanni da Matasa a cikin jerin Ministocin shugaba Buhari.

Wannan labari ya fito ne bayan wata jita-jita da aka yada ta cewar wasu daga cikin manyan gwamnonin arewa sun nuna goyon bayansu dari bisa dari ga fitaccen dan wasan domin ya zama daya daga cikin Ministocin shugaba Buhari a kasar nana.

Fitaccen jarumin dai ya nuna soyayyarsa matuka ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnatin APC, domin kuwa yana daya daga cikin jiga-jigan wadanda suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari da babbar jam'iyyar APC kamfen a yankin arewacin kasar nan.

Wasu daga cikin wadandan suka taya shugaban kasar kamfen a cikin 'yan wasan Hausan sun hada da shahararren mawakin nan Rarara, Adamu Zango, Aminu Ala, Nazifi Asnanic da sauransu
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post