Hattara tsoho! Yari ya yi wa Obasanjo wankin babban bargo kan wasikarsa ga Buhari


Legit Hausa

Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari ya cacaki tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo kan budaditar wasikar da ya rubuta ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Mista Obasanjo ya fitar da wasikar ne a ranar Litinin inda ya ke yi wa Buhari gargadi kan halin tarbarbarewar tsaro da rarrabuwar kan al'umma a kasar.

Obasanjo ya zargi shugaban kasar da nuna halin in kula kan da rashin daukan mataki kan kallubalen da suke tasowa a kasar. A sanarwar da ya fitar da hannun hadiminsa na kafafen yadda labarai, Ibrahim Dosara, Yari cacaki Mista Obasanjo da wasu shugabanin Yarabawa ta bai bayyana sunayensu ba kan sukar yadda Buhari ke tafiyar da harkar tsaro a kasar.

Tsohon gwamnan ya yi zargi tsohon shugaban kasar da yin amfani da wannan damar ne don huce fushin da ya ke fama da shi kan Buhari inda ya ce tsohon shugaban kasar bai aikata wani abin azo a gani da ta fi na Buhari ba a zamaninsa.

 "Kowa ya san cewa a zamanin Shugaba Olusegun Obasanjo ne aka yi wa mutane Zaki Biam na jihar Benue da Odi a Bayelsa kisar kiyashi. "Babban rikicin 'Yan Shi'a na Kaduna ma ta faru ne a karkashin mulkinsa. Kuma lokacin mulkinsa ne aka shuka rikin Plateau.

Kamar ya manta dukkan wadannan abubuwan da suka faru a zamaninsa. Ya kuma manta da kisar gillar da aka yi wa tsohon minista Bola Ige da jigo na jam'iyyar adawa Harry Marshall," inji shi. Ya ce babu laifi a nuna bacin rai kan kisar da aka yi wa Mrs Funke Olakunrin, diyar shugaban kungiyar Afenifere, Reuben Fasoranti, ya yi tir da yadda wasu ke sauya maganar suke cewa makiyaya Fulani ne suka aikata kisar.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post