Koyi da halayen Kwankwasiyya: Wani matashi zai fito takaran shugaban karamar hukuma a jihar Kebbi

Wani matashi dan shekara 31 Malam Mansur Abubakar Sarki, ya kuduri aniyar fitowa takaran kujeran shugaban karamar hukumar mulki ta Gwandu a jihar Kebbi bisa akidar taimakon matasa na Darikar siyasar Kwankwasiyya domin kwaikwayon kyawawan halaye, kudurori da manufofin taimakawa yayan talakawa da Dr.Rabi'u Musa Kwankwaso yake yi ga al'umma.

'Dan asalin karamar hukumar mulki ta Gwandu, Mansur, ya ce " Na yanke shawarar shiga jerin matasa da zasu tsaya takaran kujeran shugaban karamar hukumar mulki ta Gwandu ne domin nima in wanzar da irin manufa ta alhairi da zai amfani al'umma na tsawon lokaci da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya ke yi, musamman yadda ya dukufa domin aiwatar da shirinsa na daukan nauyin matasa dalibai 370 domin su je kasar waje su kara ilimi a mataki na babban Digiri na 2, watau Masters Digree".

" Bisa wannan seti da manufa da kuma tarin yawan irin wadannan ayyuka na alhairi da taimakon al'umma da Sanata Kwankwaso ya ke yi su ne suka ja ra'ayina a kan in fito fagen siyasa a matsayi na na matashi, domin in wanzar da irin wannan manufa a karamar hukumata domin matasa su amfana da tsarin a jihar Kebbi in Allah ya yarda".

Mansur Sarki, masani ne kan harkar kasuwanci, kuma mai matakin karatu na HND, ma aikaci ne a kamfanin sadarwa na wayar salula kuma gani kasheni ne kan akidar Darikar siyasa ta Kwankwasiyya a jihar Kebbi, kuma shine wanda ya assasa gidauniyar tafiyar da ilimin 'ya'ya marayu a karamar hukumar Gwandu a jihar Kebbi.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

 
Previous Post Next Post