Masu garkuwar da suka kashe wani Alhaji a Kebbi sun nemi miliyan N100 kafin sakin surukarsa

Legit Hausa
Yan bindigan da suka kashe babban dan kasuwa sannan suka yi garkuwa da surukarsa a Kebbi, sun nemi a basu naira miliyan 100 a matsayin kudin fansa kafin su sake ta.
Yan bindigan a ranar 26 ga watan Yuli, sun kashe Alhaji Yusuf Garkar-Bore, wani dan kasuwa a garin Gulma da ke jihar Kebbi, sannan kuma suka yi garkuwa da matar dansa, Aisha Yusuf.
Wani mamba na iyalan gidan wanda bai son a bayyana sunansa, ya fada wa manema labarai cewa yan bindigan sun nemi naira miliyan 100 kudin fansa daga ahlin.
“Sun kira mu sannan sun nemi sai mun biya naira miliyan 100 kafin su saki matar.
“Mun fada masu cewa bamu da irin wannan makudan ku dade sannan muka tunasar dasu lokacin da suka kai mamaya gidanmu, sun tafi da wata jaka dauke da naira miliyan daya," inji shi.
Kakakin yan sandan jihar, DSP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa basu da masaniya akan bukatar kudin fansar.
Ya Kara da cewa rundunar na kokarin ceto wacce aka sacen.
A baya Legit.ng ta rahoto ewa wasu yan bindiga dauke da makamai sun tashi garuruwa sama da 70 a jihar Sokoto, yayin da suka kashe mutane da dama tare da sace tarin dukiya da suka hada da dabbobi.
An tattaro cewa mafi akasarin mazauna garuruwan da maharan suka farmawa sun samu mafaka a manyan garuruwa, domin tsiratar da rayuwarsu.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: 
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post