Wani jirgin sojoji ya rikito bisa gidajen mutane a Pakistan

Legit Hausa
A kalla mutum 18 ne suka rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu da dama suka jikkata a sakamakon hatsarin wani karamin jirgin soji da ya fado a wata unguwa dake kusa da birnin Rawalpindi na Pakistan.
Mutum biyar dake cikin jirgin da kuma fararen hula 13 na daga cikin wadanda suka mutu a sanadiyar hatsari kamar yadda hukumar agaji ta bada labari.
Hatsarin ya faru ne a daidai lokacin da jirgin ke gudanar da atisaye. Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa ya bamu labarin cewa tun jirgin na sama kan ya fado ya soma ci da wuta.
Bayan ya fado saman gidajen sai suka kama da wuta nan take. Rahotanni sun ce jirgin samfurin King Air 350 yayi wata juyawa ne a lokacin da yake daf da inda zai sauka kwatsam sai ya fado kafin yayi saukar tasa.
Rawalpind, wadda ke kusa da babban birnin kasar Islamabad, can ne inda rundunar sojin Pakistan take da hedikwatarta, kuma jirgin mallakin sojin saman Pakistan ne.
Firai Ministan Pakistan, Imran Khan ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka rasu tare da fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata, kamar yadda gwamnatin kasar ta wallafa a shafinta na tuwita.
Wani ganau wanda al’amarin ya auku a kan idonsa ya ce, “ Jirgin ya yi hatsari ne da misalin karfe 7:00 n asafe agogon GMT, inda ya fada saman wani gida a unguwar Ghulam Khan.
“ Idona biyu lokacin da na ji wucewar jirgin ta saman gidana kuma yana ci da wuta, kafin nan kuma ya fada bisa gidan wasu mutane.” A cewar wani ganau mazaunin unguawar da hatsarin ya faru.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post