Yadda Kantoman karamar hukumar Gwandu ya jagoranci wani muhimmin lamari da kansa

Kantoman riko na karamar hukumar Gwandu a jihar Kebbi Muhammad Mode Dangiye, ya jagoranci wani aikin tsabtace gari domin inganta lafiyar al'umman garin Gwandu ta hanyar yashe Gwatoci a cikin birnin na Gwandu mai cike da tarihin Musulunci.

Mjiyar ISYAKU.COM ta ce Kantoman ya zagaya kuma aka gudanar da aikin yashe gwatocin da kansa tare da sauran jama'an gari da manyan mutane a garin Gwandu da kuma wasu jami'an Karamar hukumar. Hakazalika Kantoman ya saurari koken jama'a a Mahauta na garin Gwandu tare da alkawarin cewa zai mika kokensu ga Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu.

Bayanai sun ce ruwa kan yi ambaliya zuwa gidajjen mutane sakamakon cushewar wadannan magudanan ruwa, wanda haka ya sa Kantoman ya bukaci yashe wannan magudanan ruwan domin kauce wa sake ambaliyan ruwa zuwa gidajen jama'a.

Wani matashi mai kishin ci gaban kasar Gwandu, Malam Mansur Abubakar Sarki, ya ce " Kantoma da kanshi ya fito zuwa wajen wannan aiki, kuma ya yi daidai da ya jagoranci wannan aiki  a daidai wannan lokaci domin samar da wuri da aka yi domin wucewar ruwa, wanda haka zai sa a kauce ma ambaliya da zai iya tu'annati ga gidajen bayin Allah".

Wasu fitattun mutane da suka sami halartar wannan aiki na yashe magudanan ruwan sun hada da:

1.Rt Hon Hassan Muhammad Shallah
2. Hon Umar Usman Kambaza
3.Hon Mainasara Magaji Gwandu
4. Hon Ibrahim Riskuwa Masama
5. Hon Zaki Gora
6. Hon Atiku Ahmad Kalcha
7. Alh Bandado Muhammad ES
8. Alh Modi Alhaji Director Finance Education
9. Alh Mamuda A Mode APC Chairman
10. Alh Ibrahim Ahmad Director Social
11. Alh Babangida Maruda Wakilin Maigirma Dan Majalisar Dokokin Jahar Kebbi Hon Habibu Labbo Gwandu.
 
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post