Kan yan majalisa ya rabu game da matakin daya kamata gwamnati ta dauka a kan yan Shia

Legit Hausa


An samu cece kuce da murza gashin baki a tsakanin yayan majalisun wakilan Najeriya a yayin zamanta na ranar Talata, 23 ga watan Yuli bisa matakin daya dace gwamnati ta dauka a kan shugaban yan Shia, Ibrahim Zakzaky da mabiyansa.

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito cece kuce ya samo asali ne bayan an gabatar da wani kuduri a gaban majalisar dake bukatar gwamnatin jahar Kaduna ta saki shugaban yan Shia, Ibrahim Zakzaky.

A jawabinsa, dan majalisa daga jahar Kano, Shamsudeen Dambazau ya bayyana cewa kungiyar Shia na barazana ga tsaro da zaman lafiyar Najeriya, musamman duba da yadda suka sabbaba kisan mataimakin kwamishinan Yansanda da kuma dan jarida dake aikin bautan kasa, tare da lalata kayan gwamnati dana jama’a, don haka ya bukaci majalisar ta bayyana Shia a matsayin kungiyar yan ta’adda.

Yayin dan majalisan PDP daga jahar Oyo, Stanlye Olajide ya nemi gwamnati ta yi tattaunar sulhu da kungiyar, shi kuwa dan majalisa daga jahar Akwa Ibom, Luke Onofiok kira yayi ga majalisar ta gayyato shuwagabannin tsaro domin su bayyana musu kalubalen da suke fuskanta wajen shawo kan lamarin yan Shia.

Shima jagoran majalisa, Ado Doguwaya bayyana bacin ransa game da yan Shia, inda yace shi da kansa ya tattauna dasu tare da alkawarin zai mika bukatunsu ga majalisar, amma washegari suka kai hari ofishin jami’an tsaron majalisa suka lalata motocin mutane.

Bayan doguwar muhawara ta kusan awanni 2, kaakakin majalisa, Femi Gbajabiamila ya nemi yan majalisa su yi zabe don sanin matakin da majalisa za ta dauka, inda ya nemi ayi amfani da murya, yan Eh, da yan A’a, amma abin ya ci tura sakamakon an yi kunnen doki.

Sai ya bukaci masu Eh, su koma gefe daya, masu A’a kuma su tsaya a bangare guda, hakan ma bai yiwu ba saboda a yayin da ake sauya bangare sai kaakakin ya dakatar dasu, ya sallami yan jaridu domin su shiga ganawar sirri.

Fitowarsu daga ganawar sirrin keda wuya sai majalisar ta sanar da wata kwamitin bincike na wucin gadi wanda za ta tattauna da bangaren zartarwa domin shawo kan wannan matsalar, a karkashin jagorancin Ado Doguwa.

DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post